27 Janairu 2016 - 09:40
Shugaba Buhari zai kai ziyara Kenya

A yau Laraba ne ake sa ran Shugaban Nigeria Muhammadu Buhari zai soma wata ziyara ta kwana uku a kasar Kenya.

A yayin ziyarar shugaba Buharin zai gana da Shugaba Uhuru Kenyatta a kebe, kafin a yi wata tattaunawa kan huldar cinikayya da aikin gona da yawon bude ido tsakanin jami'an gwamnatin kasashen biyu.

Kazalika, ana kuma sa ran shugaba Muhamadu Buharin zai wuce kasar Habasha domin halartar taron shugabannin kungiyar tarayyar Afrika, wato A.U.

Tun bayan darewarsa mulki, shugaba Buhari ya kai ziyara kasashe daban-daban domin karfafa alakar da ke tsakaninsu da Najeriya da kuma kulla dangantakar kasuwanci.288